Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane a kalla 10 sun mutu sakamakon wani hari da aka kaiwa jandarmomi a arewacin Burkina Faso
2020-01-03 10:04:08        cri
A kalla mutane 10 ne suka gamu da ajalinsu a daren ranar Talatar da ta gabata, sakamakon wani harin da aka kaiwa wurin da aka girke jandarmomi a Djibo dake arewacin lardin Soum na kasar Burkina Faso.

Wasu majiyoyin tsaron sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, daga cikin wadanda aka kashe sun hada da maharan da kuma wani jandarma.

Harin na zuwa ne, yayin da shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, ke yiwa 'yan kasar jawabi a ranar Talata da dare, inda ya bayyana tabbacin samun galaba a matsalar ta'addancin dake addabar kasar.

Daga shekarar 2015 zuwa wannan lokaci, hare-haren ta'addanci sun halaka rayukan mutane sama da 700, ciki har da sojoji 200, baya ga dubban mutane da suka rasa matsugunansu a cikin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China