Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 14 sun mutu sakamakon fashewar abubuwa a arewacin Burkina Faso
2020-01-05 16:37:03        cri
A kalla mutane 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Asabar, ciki har da wasu dalibai 7, a yankin Toeni, dake Sourou, a arewa maso yammacin kasar Burkina Faso a lokacin da wata motar fasinjoji ta taka abubuwan fashewar, gwamnatin kasar Burkina Faso ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwar da ta fitar da yammacin ranar Asabar.

Saanarwar ta ce, da safiyar ranar Asabar, wasu motocin bus guda uku sun taso daga Toeni zuwa Tougan suna dauke da fasinjoji 160, daya daga cikin motocin bus din ta bi takan wasu abubuwan fashewa.

Baya ga rasuwar mutanen 14, akwai kuma wasu mutanen 19 da suka samu raunuka, uku daga cikinsu suna cikin yanayi mai tsanani, inda aka garzawa da su asibiti don bas u kulawa, in ji sanarwar.

Gwamnatin kasar ta yi Allah wadai da babbar murya kan wadannan masu kai hare-haren matsorata wadanda ke keta hurumin jama'a.

A shekarar da ta gabata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi a kasar sun haddasa rudanin addini da na kabilanci a kasar Burkina Faso, musamman a shiyyar arewacin kasar dake makwabtaka da Mali. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China