Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojoji a kalla 11 sun mutu a sakamakon harin da aka kaiwa sojojin kiyaye tsaron kasar Burkina Faso
2019-12-26 09:49:32        cri
Bisa labarin da ma'aikatar kiyaye tsaron kasar Burkina Faso ta bayar a daren ranar 25 ga wata, an kai hari ga sojojin kiyaye tsaron kasar a arewa da tsakiyar kasar a wannan rana yayin da suke yin sintiri, wanda ya haddasa mutuwar sojoji a kalla 11.

Wani jami'in ma'aikatar ya bayyana cewa, wasu dakaru sun kai hari ga sojojin kiyaye tsaron kasar a wani kauye dake yankin arewa da tsakiyar kasar, wanda ya haddasa mutuwar sojoji a kalla 11 tare da bacewar sojoji da dama.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Burkina Faso suka bayar, an ce, sojojin kiyaye tsaron kasar sun mayar da martani bayan da aka kai hari gare su, sun kuma harbe dakaru 5 har lahira.

A ranar 24 ga wannan wata, bangaren soja da gwamnatin kasar Burkina Faso sun bayar da labari cewa, wasu dakaru sun kai hari ga sojojin kiyaye tsaro da fararen hula a wannan rana a jihar Soum dake arewacin kasar, wanda hakan ya haddasa mutuwar sojoji 7 da fararen hula 35. Sojojin kiyaye tsaron kasar sun harbe dakaru 80 har lahira yayin da suke yin musayar wuta. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China