Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin kasar Sin da nahiyar Turai
2020-02-18 12:19:07        cri
Da safiyar jiya Litinin ne, aka komo da ayyukan dakon kaya ta jirgin kasa mai lamba X8059, wanda zai tashi daga birnin Shenyang dake arewa maso gabashin kasar Sin zuwa nahiyar Turai. Jirgin mai dauke da kayan injuna, da na kananan masana'antu, zai isa Moscow, babban birnin kasar Rasha bayan kwanaki 18.

An yi hasashen cewa, akwai jiragen kasa guda bakwai wadanda za su tashi daga kasar Sin zuwa nahiyar Turai a wannan sati, domin fara zirga-zirga kamar yadda ya kamata. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China