Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta ce arewa maso yammacin Syria na cikin wani yanayi mafi tayar da hankali
2020-02-29 16:04:03        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce hare-haren baya bayan nan da ake kaiwa yankin arewa maso yammacin Syria dake hannu 'yan adawa, daya ne daga cikin yanayi mafi tayar da hankali da aka gani cikin kusan shekaru 9 da aka shafe ana rikici a kasar.

Antonio Guterres, ya ce abu mafi muhimmanci shi ne gaggauta tsagaita bude wuta kafin yanayin ya kara ta'azzarar da za a sha wuyar shawo kansa. Yana mai cewa a dukkan tattaunawarsa da masu ruwa da tsaki a rikicin, sako daya yake isarwa, wato a ja da baya domin kaucewa ta'azzarar yanayin.

Kiran na Antonio Guterres na zuwa ne, bayan rahotanni daga Syria sun nuna cewa luguden wuta da jiragen yakin Turkiyya suka yi jiya a lardin Idlib na arewa maso yammacin Syria, ya yi sanadin kashe a kalla sojojin kasar 11.

Ya bayyana yayin taron manema labarai a wajen zauren kwamitin sulhu na majalisar cewa, yana mai kara nanata bukatar kare fararen hula.

Antonio Guterres ya ce, yaki bai taba kawo komai ba face asara da bakin ciki. Yana mai cewa, babu wata mafita da za a samu daga matakan soji. Inda ya ce hanya daya tilo ita ce cimma masalaha a siyasance karkashin MDD. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China