Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da a matse kaimi wajen yaki da COVID-19 ba tare da wariya ba
2020-02-29 16:22:29        cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, yanzu ne lokacin da ya kamata gwamnatoci su matse kaimi da yin dukkan mai yuwuwa wajen yaki da COVID-19, bisa girmama 'yancin dan Adam ba tare da wariya ba.

Antonio Guterres ya ce ana samun sabbin masu kamuwa da cutar a wasu kasashe, ciki har da nahiyar Afrika. Yana mai cewa yanzu ba lokaci ne na fargaba ba, lokaci ne da ya kamata a shirya sosai don yaki da cutar.

Ya ce za a iya dakile yaduwarta, sai dai lokacin da ake da shi na yin hakan na raguwa.

Sakatare Janar din ya yi kira da hada hannu tare da goyon bayan juna tsakanin dukkan kasashen duniya, domin kowacce ta sauke nauyin dake wuyanta.

Ya ce yayin da suke hada hannu, MDD za ta ba su dukkan goyon baya, haka zalika hukumar lafiya ta duniya.

A jiya Juma'a ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta kara matakin hadarin COVID-19 a duniya, daga "mai hadari" zuwa "mai hadari sosai". (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China