![]() |
|
2020-03-04 09:37:27 cri |
Ma'aikatar lafiya ta Nijeriya, ta ce an gano mutane 100 da suka yi mu'amala da wanda aka samu da cutar COVID-19 a kasar, inda ta ce har yanzu ana aikin lalubo sauran wadanda suka yi mu'amala da shi saboda kare yaduwar cutar a Nijeriya.
Karamin ministan lafiya na kasar Olorunimbe Mamora, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, an fara lalubo mutanen ne daga jerin sunayen wadanda suka shiga jirgi daya da shi zuwa Nijeria a makon da ya gabata.
A cewarsa akwai kimanin mutane 157 da suka bi jirgin.
An fara neman mutanen ne bayan hukumomin lafiya na kasar sun tabbatar da samun bullar cutar na farko a jihar Lagos. Wanda aka samu da cutar wani dan kasar Italiya ne da ya shiga kasar domin kasuwanci a ranar 25 ga watan Fabreru.
A cewar Ministan, an gano fasinjoji 54 daga jerin sunayen wadanda suka bi jirgin, haka zalika an gano mutanen suka yi mu'amala da shi a Otel na Lagos da kuma a wurin da ya ziyarta a jihar Ogun dake kudu maso yammacin kasar, wadda ke makwabtaka da jihar ta Lagos. (Fa'iza Msutapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China