Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun halaka kimanin kauyawa 50 a Najeriya
2020-03-02 19:21:07        cri
Rahotanni daga jihar Kaduna a yankin arewacin Najeriya na cewa, jiya Lahadi 'yan bindiga sun halaka kauyawa kimanin 50, ciki har da jirarai a kananan hukumomi uku dake jihar.

Wata kafar 'yan sanda ta bayyana a yau Litinin cewa, kananan hukumomi uku da wannan lamari ya shafa, sun hada da Giwa, da Birnin Gwari da kuma karamar hukumar Igabi, dukkansu a yankin arewacin jihar ta Kaduna.

Majiyar ta shaidawa manema labarai cewa, 'yan bindigar sun farma kauyuka shida dake wadannan yankuna uku. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China