Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamna a Najeriya ya bada tabbacin 'yan bindiga sun kashe mutane 50 a wasu kauyuka
2020-03-03 09:49:18        cri
Kimanin mutane 50 'yan bindiga suka kashe a wasu kauyuka a kananan hukumomi biyu a jahar Kaduna a Najeriya da safiya ranar Lahadi, gwamnan jahar Nasir El-Rufai ya tabbatar da faruwar lamarin.

Gwamnan, wanda ya ziyarci kananan hukumomin biyu, Igabi da Giwa, ya nanata cewa ba zai taba yin sulhu da 'yan bindigar ba.

Ya ce ba don sojojin Najeriya na sama da na kasa suna kaddamar da hare hare kan 'yan bindigar ba da lamarin ya fi haka muni.

Gwamnan ya baiwa dangi da iyalan mutanen da aka kashe tabbacin kamo maharan kuma za'a gurfanar da su gaban shari'a.

El-rufai ya ce tuni aka yi jana'izar mutanen da suka mutu kamar yadda addinin musulunci ya tanada. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China