Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta jinjinawa kasar Sin kan kokarin da take yi na dakile cutar COVID-19
2020-03-01 17:19:48        cri

Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, gwamnatin Nijeriya da ma al'ummarta daga bangarori daban daban sun jinjinawa kasar Sin kan kokarin da take yi wajen dakile cutar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a sanarwar da ya bayar, ya bayyana cewa, kasar Sin ta zama abin koyi a kokarin da take yi na dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da ma yadda take mu'amala da hadin gwiwa da kungiyoyin kasa da kasa da sauran kasashen duniya.

Ministan kiwon lafiya na kasar Osagie Ehanire shi ma ya bayyana cewa, bayan barkewar cutar, kasar Sin ta dauki jerin matakai masu inganci, ta bayyanawa duniya halin da take ciki ba tare da rufa rufa ba, ta kuma yi hadin gwiwa da kasa da kasa, matakin da ba kawai ya amfanawa kanta ba ne, har ma da duniya baki daya. Shi ya sa ta samu yabo daga hukumar lafiya ta duniya da kuma kasa da kasa.

Ban da haka, shugaban kwamitin hukumar zartaswar kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka(ECOWAS) ya ce, kasar Sin tana daukar kwararan matakai na dakile cutar, kuma kungiyar ECOWAS ta yaba da matakan da kasar Sin ta dauka, kuma ta nuna cikakken goyon bayanta ga kasar Sin da al'ummarta. Ya ce, tabbas ne kasar Sin za ta samu galabar yaki da cutar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China