Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dattawan Amurka ta yi watsi da batun tsigewa Donald Trump daga mukaminsa
2020-02-06 11:00:08        cri

Jiya Laraba, kwamitin majalisar dattawan kasar Amurka, mai kula da batun daftarin da ya bukaci a tsige shugaba Donald Trump daga mukamin sa, ya kada kuri'u game da batun, inda daga karshe ki amincewa da ayoyin biyu da aka gabatar, masu nasaba da sauke Trump daga kujerar shugabancin kasar. An ce ba bu tabbaci game da ko Trump ya aikata laifin da ake zargin sa ko a'a, don hakan ba za a iya yanke hukuncin sauke shi daga mukamin sa ba.

A wannan rana da yamma, majalisar dattawan kasar ta gabatar da sakamakon jefa kuri'u kan ayar korar Trump, bisa laifin yin amfani da ikonsa yadda yake so, inda 52 suka ki amincewa, wasu 48 kuma suka nuna amincewar su. Ban da wannan kuma, a kan ayar korar sa bisa laifin kawo cikas ga ayyukan majalisar dokokin kasar, 53 sun jefa kuri'un rashin yarda, kana 47 sun amince da kudurin.

'Yan majalisun da suka kada kuri'un dai sun goyi bayan bangaren da jam'iyyar su ta karkata. Daga karshen dai ba a tabbatar da laifin da ake zargin Trump da aikatawa ba, wanda hakan ya sa ba za a sauke shi ba, kuma an kawo karshen wannan batu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China