![]() |
|
2020-02-26 11:59:32 cri |
Da yake jawabi ga 'yan jaridu bayan tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump, firaministan Indiya Narendra Modi, ya bayyana cewa, shi da Trump sun yanke shawarar bin hanyoyin da shari'a ta tanada wajen cimma matsaya wanda tuni ministocin kasuwanci na kasashen biyu sun riga sun fara tattaunawa kan batun.
Da ma dai shugaba Trump ya sha nanata zarge-zarge da yake yiwa wasu kasashen duniya game da aiwatar da tsarin manufar ba da kariyar ciniki, kuma ya sha zargin Indiya inda ya ayyanata a matsayin "Shugabar haraji" sakamakon yadda take sanya haraji mai tsanani kan kayayyakin Amurka. Ya sha rokon Modi da ya rage yawan harajin da kasar ke karba kan baburan da kamfanin Harley Davidson ke sayarwar kasar a matsayin tukuici.
A cewar rukunin kamfanonin watsa labarai na Indiya, wakilan tattaunawar Amurka sun fice daga zauren taron tattaunawa a sa'o'in karshe, inda suka sanar da Indiya cewa, ta jira zuwa babbar yarjejeniya da za'a gudanar nan gaba.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China