Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya duba yadda ake gudanar da aikin binciken kimiyya, asali da maganin COVID-19
2020-03-02 19:49:31        cri
A yau Litinin da rana ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci wasu cibiyoyin guda biyu a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda yake gudanar da aikin binciken kimiyya game da cutar COVID-19 da gano asali da maganin cutar.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin kolin sojojin kasar, ya ziyarci cibiyar kimiyyar likitanci ta soja da makarantar nazarin aikin likitanci ta jami'ar Tsinghua, domin ganin irin ci gaban da aka samu a fannin samar da allurar riga-kafin cutar, kwayoyin garkuwar jiki, da magani da na'urorin binciken da ake amfani da su.

Xi ya yabawa masana da masu binciken, ya kuma jagoranci taron karawa juna sani, inda ya saurari ra'ayoyi da shawarwari daga jami'an sassan da abin ya shafa gami da masu bincike.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China