Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Yadda kasashen Afirka suka goyi bayan yadda kasar Sin take yaki da COVID-19 ya nuna dangantakar abokantakar dake tsakaninsu
2020-02-26 10:21:26        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yadda kasashen Afirka da al'ummominta suka goyi bayan kasar Sin ta fannoni daban-daban kan yadda take yaki da cutar numfashi ta COVID-19, ya nuna yadda kyakkyawar dangantakar abokantaka ta tsayawa da taimakawa juna tsakanin Sin da Afirka.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, yayin tattaunawa ta wayar tarho da firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed. Yayin tattaunawar, Xi ya yaba da imanin da kasar Habasha ke da shi kan kasar Sin, yayin da kasar ke ci gaba da yin mu'amala da musaya tsakaninta da kasar Sin kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawara.

Xi ya tuna cewa, a shekarar 2014, gwamnati da al'ummar Sinawa sun taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da cutar Ebola da ta barke, inda kasar Sin ta kasance a kan gaba wajen ba su tallafi, duk da wahalhalu da hadurra dake tattare da yin haka. Ya ce, a wannan karo, kasashen Afirka da al'ummarta, sun goyi bayan kasar Sin ta fannoni daban-daban a yakin da take yi da cutar COVID-19, abin da ke nuna dangantakar abokanta na tsayawa da taimakawa juna tsakanin Sin da Afirka.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, su ma kasashen Afirka, suna fama da manyan kalubale a fannin kandagarki da hana yaduwar cututtuka, a don haka, a shirye kasarsa ta ke ta taimaka musu da kayayyakin kiwon lafiya da ake matukar bukata, ciki har da na'urorin gwaje-gwaje.

A nasa bayani firaminista Abiy Ahmed, ya ce, a madadin gwamnati da al'ummar kasar Habasha, yana mika jaje ga daukacin al'ummar Sinawa game da annobar COVID-19 da ta bulla a kasar, ya kuma yaba da managartan matakan da kasar Sin ta dauka a kan lokaci na ganin bayan wannan cuta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China