Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya amsa wasikar da Bill Gates ya aike masa dangane da cutar COVID-19
2020-02-22 15:31:30        cri

Bayan samun wasika daga hamshakin dan kasuwar Amurka, kuma daya daga cikin shugabannin gidauniyar Bill & Melinda Gates, wato Bill Gates dangane da cutar COVID-19, shugaba Xi Jinping ya aike masa da amsa.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan wata 20 ga watan Fabreru, shugaba Xi Jinping ya yi matukar godiya ga yunkurin Gidauniyar Bill & Melinda Gates da kuma wasikar goyon baya da hamshakin dan kasuwar ya aike ga al'ummar Sinawa a wannan muhimmin lokaci.

A wasikarsa mai dauke da kwanan wata 6 ga watan Fabreru, Bill Gates ya ce gidauniyarsa ta sadaukar da dala miliyan 100 cikin asusun ba da agajin gaggawa, wanda galibinsa za a yi amfani da shi wajen taimakawa kasar Sin karfafa nazarin cututtuka da ba da daukin gaggawa da bincike da samar da magunguna da riga kafi da kuma duba marasa lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China