Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi Jinping ya yi jawabi a gun taron karfafa gwiwar yaki da cutar COVID-19 da raya tattalin arzikin Sin
2020-02-23 20:52:53        cri
An kira taron karfafa gwiwar aikin yaki da kuma kandagarkin cutar COVID-19 da raya tattalin arzikin al'ummar kasar Sin a yau Lahadi a nan birnin Beiing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da bada jawabi.

A cikin jawabinsa, ya jadadda cewa, Sin ta shawo kan walalhalu da dama a tarihinta, amma wadannan wahalhalu ba su lahanta ta ba ko kadan, a maimakon haka, ta samu karfi, kuma ta samu farfadowa daga wadannan matsaloli.

Ya zuwa yanzu, ana fuskantar mawuyacin hali mai tsanani, kuma ana cikin wani muhimmin lokaci na yaki da yin kandagarki kan wannan mumunar cuta, kamata ya yi, kwamitocin matakai daban daban na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma gwamnatocin wurare daban-daban su kara imaninsu da ci gaba da gudanar da aikin kandagarkin yadda ya kamata.

Ya kara da cewa, kamata ya yi a kara karfinsu wajen dawo bakin aiki da maido da zaman oda da doka, har ma da kara karfin manufofin daidaita, ta yadda za a yi amfani da boyayyen karfi mai inganci a kasar Sin, don cimma muradun raya tattalin arzikin kasar a wannan shekara. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China