Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dattawan Najeriya ta goyi bayan kasar Sin wajen yaki da cutar numfashi
2020-02-20 13:07:34        cri

Kwanan baya, shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattawan kasar Najeriya Adamu Bulkachuwa, ya aike da wasika ga kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda a madadin majalisar dattawan, ya jajanta, da goyon baya ga kasar Sin, a aikin ta na yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Adamu Bulkachuwa ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen yaki da cutar numfashin, ciki har da matakan da ta dauka na sanya mutane masu yawa zama, da aiki a gidajensu, domin hana yaduwar cutar, kuma duk duniya na nuna yabo, kan matakan yaki da cutar da kasar Sin ta dauka.

Sai dai duk da haka, kwanan baya an samu wasu lamuran dake nuna kyama ga kasar Sin a wasu kasashen yamma bisa dalilin annobar, ya ce "mun zargi wadannan matakai sosai. Majalisar dattawan Najeriya da kwamitin kula da harkokin wajen majalisar, suna tsaye tare da Sinawa, suna nuna iyakacin kokarin su na goyon bayan bangaren Sin a fannin yaki da cutar, za kuma su yi duk mai yiwuwa don tallafa wa kasar ta Sin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China