![]() |
|
2020-02-28 12:04:38 cri |
A nasu jawabin, mahalarta taron, sun jinjina kwararan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka na shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, da babbar gudummawa da sadaukarwar da kasar ta bayar ga inganta harkokin kiwon lafiyar duniya baki daya. Sun kuma bayyana cewa, gwamnati gami da jama'ar tarayyar Najeriya na zama kafada da kafada da kasar Sin, suna kuma da yakinin cewa Sin za ta iya shawo kan annobar cutar nan da nan.
Har wa yau, sun ce, kasar Sin ta yi abin al'ajabi wajen samun ci gaba ta hanyar shugabanci nagari da tsarin kasar mai inganci, inda a ganinsu, tsayawa kan daidaita matsaloli bisa hakikanin halin da ake ciki a kasar ita ce mafita. Najeriya na fuskantar matsalolin da suka kunshi yawan jama'a da kuma rashin samun guraban ayyukan yi, a don haka ya kamata ta koyi wasu dabarun kasar Sin a fannonin da suka shafi inganta rayuwar al'umma, da raya sana'o'in dake bukatar daukar ma'aikata masu yawa, da kuma kara bada fifiko kan samar da guraban ayyukan yi ga al'ummar kasar.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China