Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya: an tabbatar da mutumin farko da ya kamu da annobar COVID-19
2020-02-28 13:24:56        cri
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Nijeriya ta tabbatar da wani mutum da ya kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a jihar Lagos a ranar 27 ga wata, wanda shi ne na farko da aka tabbatar ya kamu da annobar a Nijeriya bayan barkewar annobar a kasar Sin a watan Janairun bana.

Dan kasar Italiya da ya kamu da cutar, yana aiki ne a Nijeriya, ya koma Lagos daga birnin Milan na Italiya a ranar 25 ga wata. Dakin gwaje-gwaje na sashen nazarin kwayoyin cuta na asibitin jami'ar Lagos ya tabbatar da cewa, mutumin ya kamu da annobar. Yanzu haka yana samun jiyya a asibitin shawo kan cututtuka masu yaduwa a Yaba da ke Lagos, kuma ba ya cikin hali mai tsanani.

Gwamnatin Nijeriya tana inganta matakanta na kandagarki da dakile yaduwar annobar. Cibiyar kandagarki da hana yaduwar annoba ta Nijeriya NCDC tana jagorantar hukumomin yaki da cutar COVID-19 wajen daukar matakan gaggawa, za kuma ta hada kai da hukumar lafiya ta Lagos don daidaita barkewar annobar da kuma daukar matakai.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China