Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Najeriya ce ta daya a yawan mutanen da suka kamu da cutar takin fuka a Afirka
2020-02-28 10:55:10        cri
Alkaluman da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar na nuna cewa, Najeriya ce ta daya a yawan mutanen da suka kamu da cutar tarin fuka a nahiyar Afirka, kana kasar dake cikin kasashen goman farko a duniya.

Wakiliyar hukumar ta WHO a nahiyar Afirka, Tereza Kasaeva, wadda ta bayyana hakan yayin da ta jagoranci wata tawaga a lokacin da ta ziyarci shugaban majalisar dattawan Najeriya a Abuja, fadar mulkin kasar, ta bayyana cewa, cutar ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutane miliyan 1.5 a duniya a shekara.

Kaseava ta yi kira ga gwamnatin Najeriya, da ta kara samar da kudade a ayyukan kiwon lafiya a matakin farko, ta hanyar daukar matakan gaggawa a bangaren majalisar dokokin kasar.

A cewar jami'ar, hukumar WHO za ta ci gaba da amfani da duk wasu matakan ta na fadakar da jama'a, don kara samar wa Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka da kudade da tsare-tsaren da ake bukata, yayin da ta ke kokarin ganin bayan cutar tarin fuka a fadin kasar nan da shekarar 2030.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China