Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na hada kai da Japan da Koriya ta Kudu wajen yaki da annoba
2020-02-28 12:42:22        cri
Zhao Lijian, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana Jiya Jumma'a cewa, kasar Sin na lura da yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Koriya ta Kudu da Japan. Kuma Kasar Sin ta godewa gwamnatocin kasashen 2 da jama'arsu sosai, dangane da goyon baya da taimakon da suka ba ta wajen yaki da annobar. Ya ce Sin ta fahimci yadda kasashen 2 suke yaki da annobar sosai, kuma akwai kyakkyawar alakar makwabtaka tsakanin kasashen 3, kana suna da makoma iri daya wajen yaki da annobar, don haka Kasar Sin za ta ba da nata taimako ga Koriya ta Kudu da Japan.

Kakakin ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Sin na son hada kai da Koriya ta Kudu da Japan wajen kyautata tsarin ko-ta-kwana na tuntubar juna kan yaki da annoba, da kara yin musayar bayanai da fasahohin yaki da annoba, da dabarun ba da jiyya, da nazarin allurar rigakafi da dai sauransu. Ya ce Sin tana son hada gwiwa da kasashen 2 wajen tsaurara matakan yaki da annobar a tasoshin bincike a iyakokin kasa, da kara karfin yin bincike, da rage tafiye-tafiye zuwa ketare da ba su wajaba ba.

Zhao Lijian ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta shiga mataki mafi muhimmanci wajen yaki da annobar, amma za ta yi iyakacin kokarinta wajen taimaka wa Koriya ta Kudu da Japan, yana mai cewa, Kasashen 3 za su taimaka wa juna wajen yaki da annobar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China