Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suke warkewa daga cutar COVID-19 ya zarce na sabbin wadanda suke kamuwa Sin cikin kwanaki 10 a jere
2020-02-28 10:00:21        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta bayyana a yau Juma'a cewa, adadin wadanda suke warkewa daga cutar COVID-19 a babban yankin kasar, ya zarce adadin sabbin wadanda ke kamuwa da cutar, cikin kwanaki 10 a jere.

A cewar hukumar, a jiya Alhamis, an sallami mutane 3,622 daga asibiti bayan sun warke, a babban yankin kasar, adadin da ya zarce 327, na sabbin wadanda suka kamu da cutar.

Ya zuwa jiya Alhamis, jimilar mutane 36,117 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar numfashi ta COVID-19.

A jiya, adadin wadanda suka warke a lardin Hubei da Wuhan, babban birnin lardin, shi ma ya zarce na sabbin wadanda suka kamu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China