Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun kashe mutane 30 a arewa maso yammacin Najeriya
2020-02-17 10:12:57        cri
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce, wasu 'yan bindiga a kan babura sun kai hari kan wasu kauyuka biyu, inda suka kashe mutane 30 a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

A wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, jami'in dan sandan jahar Katsina ya ce, maharan sun kaddamar da hare-hare kan kauyukan Tsauwa da Dankar dake karamar hukumar Batsari a jahar Katsina a daren Jumma'ar da ta gabata.

Gambo Isah, shi ne kakakin hukumar 'yan sandan jahar Katsina ya ce, 'yan bindigar sun kai harin kan babura a kauyukan biyu inda suka bude wuta kan mazauna kauyukan, ya kara da cewa, galibin wadanda aka kashe tsoffi ne masu yawan shekaru da kananan yara wadanda ba za su iya gudu don tsira da rayukansu ba.

Kimanin mutane 21 aka kashe a kauyen Tsauwa inda maharan suka kone gidaje masu yawa kana suka yi awon gaba da kayan abinci. Sannan maharan sun kashe wasu mutanen 9 a kauyen Dankar, in ji kakakin 'yan sandan.

Gambo Isah ya ce, hukumar 'yan sandan tana aikin hadin gwiwa da sojoji, inda ta samu nasarar kama mutum guda da ake zargi tare da gano babura 9 mallakin 'yan bindigar wadanda suka yi amfani da su wajen kaddamar da hare-haren. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China