Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun kasashe 37 sun rubuta wasikar mara baya ga nasarorin kare hakkin dan Adam na kasar Sin
2019-07-13 16:55:22        cri
Jakadun kasashe 37 sun aike da wasika ta hadin gwiwa ga shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD da babbar kwamishinar ofishin MDD dake kare hakkin dan Adam, domin nuna goyon bayansu ga dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin.

Cikin wasikar ta hadin gwiwa, jakadun sun ce suna yabawa nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam ta hanyar rungumar akidar samar da ci gaba domin moriyar al'umma da kuma karewa da inganta hakkin dan Adam ta hanyar ci gaba.

Sun kara da cewa, suna godewa gudunmowar da kasar Sin ke bayarwa ga yunkurin kare hakkin dan Adam a duniya.

Jakadun sun kuma bayyana adawarsu ga wasu kasashen dake siyasantar da batun kare hakkin dan Adam ta hanyar kunyatawa da matsawa wasu kasashe lamba.

Wasikar na dauke da sa hannun jakadun kasashen 37 dake ofishin MDD na Geneva. Kasashen sun hada da Rasha da Pakistan da Saudiyya da Masar da Algeria da Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar da Nijeriya da Angola da Togo.

Sauran sun hada da Tajikistan da sauran kasashen Asiya da Afrika da kuma Gabas ta Tsakiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China