Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron tabbatar da kare hakkin dan Adam na kananan kabilun kasar Sin
2019-07-03 10:15:50        cri

A yayin taro na 41 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, hukumar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta gudanar da taron tabbatar da kare hakkin dan Adam na kananan kabilu na kasar Sin a birnin Geneva a jiya, inda masanan hukumar sun yi bayani game da halin tabbatar da hakkin dan Adam na kananan kabilun kasar Sin a fannoni daban daban.

Mataimakiyar babban sakataren hukumar dake shugabancin taron Wang Linxia ta yi nuni da cewa, a cikin shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, Sin ta dora muhimmanci ga tabbatar da hakkin kananan kabilun kasar, da tsara dokokin tabbatar da moriyarsu, da aiwatar da su yadda ya kamata. Kana an kyautata tsarin bada tabbaci ga kare hakkin dan Adam na kananan kabilun kasar, hakan an samu babban ci gaba kan sha'anin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi. Sin ta fitar da tsarin ikon aiwatar da harkokin yankunan kabilu da kansu bisa halin da ake ciki a kasar, hakan ya tabbatar da hakkin dan Adam na kananan kabilu a fannonin siyasa, zamantakewar al'umma, tattalin arziki, al'adu, samun bunkasuwa da sauransu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China