Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki na manyan jam'iyyun Amurka a Iowa
2020-02-04 11:30:14        cri
Kusoshin jam'iyyun Democrat da Republican na Amurka, sun gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki a jihar Iowa a daren jiya Litinin, a wani bangare na shirye shiryen fitar da 'yan takarar shugabancin kasar na shekarar 2020.

Kusoshin jam'iyyun biyu sun fara tarukan na jiya ne, da misalin karfe 7 na almuru bisa agogon GMT. Taron ya hallara dubban masu rajistar jam'iyyun a majami'u, da dakunan karatu, da filayen wasannin makarantu jihar, domin tattauna matsayar su game da wanda ya fi dacewa su matawa baya, a matsayin dan takara yayin zaben dake tafe.

A bangaren jam'iyyar Republican mai mulkin Amurka, shugaba Donald Trump ne ake hasashen zai samu amincewar kusoshin jam'iyyar ta sa, a wani tsari na kada kuri'u da 'yan jam'iyyar ke gudanarwa, na nuna goyon bayan su ga wanda zai yiwa jam'iyyar takara, kamar yadda hakan ta faru a shekarar 2016, inda ya samu amincewar su da kaso 9.5 bisa dari.

Sabanin jam'iyyar Republican, 'yan jam'iyyar Democrat na nuna goyon bayan su ga dan takara ne, ta hanyar komawa wani bangare da aka kebe ga 'yan takara daban daban. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China