2020-02-28 21:11:59 cri |
A yau Juma'a ne firaministan Sin Li Keqiang, ya yi kira ga masu binciken kimiyya, da su kara azama, wajen cimma manyan nasarori, a fannin kimiyyar likitanci, yayin da ake ci gaba da yaki da cutar numfashi ta COVID-19.
Li Keqiang ya ce yana fatan za a kara zage damtse, wajen samar da sinadarar da za su rika taimakawa aikin gano cutar, da wadanda za a yi amfani da su wajen rigakafin cutar.
Li ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake rangadi a cibiyar kasa ta ayyukan gaggawa, mai aikin samar da magunguna da kayayyakin yaki da cutar ta COVID-19. (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China