Shugabannin kasar Sin sun samar da kudi kyauta domin aikin yaki da cutar COVID 19
Zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya kira wani taro a yau Laraba karkashin jagorancin shugaban kasar Xi Jinping, inda aka nazarci halin da ake ciki, don tunkarar aiwatar da muhimman ayyukan kandagarki, da shawo kan cutar COVID 19.
Shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi yayin taron, inda aka samu halartar sauran zaunannen mambobin ofishin, ciki hadda firaminista Li Keqiang. Shugabannin sun kuma ba da kudin kyauta ga aikin yaki da cutar bisa kiran da kwamitin kolin jam'iyyar ya yi wa dukkan 'yan jam'iyyar.
A cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya ce matakai masu fa'ida da ake dauka, domin kandagarki da kuma shawo kan cutar na kara fadada, kuma fannonin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma na kara farfadowa, amma fa yanayin da ake ciki a lardin Hubei, da birnin Wuhan, fadar mulkin lardin na ci gaba da kasancewa mai sarkakiya, da kuma tsanani, don haka ba za a kau da kai ga yiwuwar sake fantsamar annobar zuwa wasu sauran yankuna ba.
Shugaba Xi ya ce a wannan gaba, yana da muhimmanci a dage, wajen tabbatar da an dakile yaduwar cutar, a kuma gaggauta gudanar da dukkanin ayyuka, na raya tattalin arziki da bunkasa zamantakewar al'umma (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba