Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da tsare tsaren tallafawa sana'o'in raya al'adu da yawon shakatawa da cutar COVID-19 ta shafa
2020-02-26 19:54:10        cri

Mahukuntan kasar Sin, sun fitar da jerin matakai da za su tallafawa masu gudanar da sana'o'in raya al'adu da yawon shakatawa da suka jigata, sakamakon bullar cutar COVID-19, wadda ta tilasta dakatar da hada hada.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a yau Laraba, jami'i a ma'aikatar raya al'adu da yawon shakatawa na kasar Sin Liu Kezhi, ya ce dakatar da hada hada a wadannan sassa, ya taimaka matuka wajen dakile yaduwar cutar, to sai dai kuma ya jefa masu wadannan sana'o'i cikin matsanancin yanayi.

Jami'in ya ce ma'aikatar cinikayya ta fara aiki tare da wasu ma'aikatun gwamnati, domin samar wa wadannan sassan sana'o'i agaji na kudaden musamman, da tsarin biyan haraji, da na hada hada, da matakan rage musu kashe kudade, da sauran hidimomi na ba da hidima da suke bukata, ta yadda za su samu farfadowa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China