2020-02-28 17:04:44 cri |
Rahotanni daga hukumar sa ido kan harkokin bankuna da bada inshora ta lardin Zhejiang na kasar Sin sun ce, domin rage illar da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ke haifarwa, lardin na himmatuwa wajen tallafawa masana'antu kananan matsakaita ta fannin hada-hadar kudi, wato ko da kamfanonin ba su mayar da kudin da aka ba su aro a karon da ya gabata ba, za su iya ci gaba da neman rance. Kawo yanzu akwai kamfanoni sama da dubu 200 wadanda suka ci gajiyar wannan kyakkyawar manufa domin haye wahalhalun da suke fuskanta.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China