Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan sabbin mutanen da suka warke daga cutar COVID-19 ya ninka yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a kwanaki 8 a jere
2020-02-26 13:23:58        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, yawan sabbin mutanen da suka warke daga annobar cutar numfashi ta COVID-19 ya ninka yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a cikin kwanaki 8 a jere.

A ranar Talata mutane 2,422 ne aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar a kasar Sin, wanda ya ninka adadin mutanen da suka kamu da cutar a wannan rana, yawan mutanen da suka kamu da cutar 406 ne, a cewar hukumar lafiyar.

Baki daya mutane 29,745 ne aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar ya zuwa ranar Talata.

A cewar alkaluman hukumar lafiyar, adadin sabbin mutanen da suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19 a lardin Hubei da hedkwatar lardin wato Wuhan ya ninka yawan sabbin wadanda suka kamu da cutar a ranar Talata.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China