Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kira da a kara azama kan tafiyar da harkokin kiyaye hakkin dan Adam cikin adalci
2020-02-28 16:04:27        cri

Taro karo na 43 na kwamitin kula da harkokin kiyaye hakkin dan Adam na MDD, ya shirya taron mu'amala kan rahoton babbar hukumar MDD mai kula da hakkin dan Adam da dai sauransu a jiya Alhamis, inda Liu Hua, wakilin kasar Sin mai kula da hakkin dan Adam ya wakilci kasashen da ke da ra'ayi kusan iri daya dangane da batun, ya kuma yaba da yadda Madam Michelle Bachelet, babbar jami'ar MDD mai kula da hakkin dan Adam ta mai da hankali kan tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Kana ya yi fatan za ta kara sauraron kasashe mambobin kwamitin, musamman ma kasashe masu tasowa, wajen ci gaba da kara azama kan kare hakkin dan Adam cikin adalci.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China