Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin MDD sun bukaci a samar da kudaden yaki da farin dango
2020-02-26 10:23:21        cri
Darakta janar na hukumar aikin gona da samar da abinci ta MDD (FAO), da babban jami'in MDD mai kula da fannin jin kan bil Adama da ba da agajin gaggawa, da babban daraktan hukumar kula da shirin samar da abinci na kasa da kasa (WFP), sun bukaci a samar da karin kudaden ayyukan yaki da farin dango, a cewar sanarwar kakakin MDDr.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce a ranar 20 ga watan Janairu, FAO ta nemi a samar da kudi dala miliyan 76 domin aikin yaki da farin dango, amma hukumar tace ana samun tafiyar hawainiya wajen samun kudaden da ake bukata na shirin yaki da annobar farin.

Jami'an sun bayyana cewa tun daga wancan lokaci, matsayar bazuwar farin dangon tana ci gaba da ta'azzara a dukkan shiyyar gabashin Afrika, a halin yanzu, kudaden da ake bukata na shirin sun ninka, inda ya tasamman dala miliyan 138, a cewar Dujarric. WFP ya yi gargadin cewa, kudaden da ake bukata a yanzu wajen kai dauki kan barnar da farin dangon ya haifar na karacin abinci ya ninka har sau 15 na yawan kudaden da ake bukata don yin rigakafin hana yaduwar farin dangon.

Ya kara da cewa, kawo yanzu, dala miliyan 33 kacal aka samu daga cikin adadin da ake bukata.

Shiyyar gabashin Afrika tana fuskantar mummunan ibtila'in farin dango da ba'a taba ganin irinsa ba cikin gwamman shekaru.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China