Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD ta shirya taron tunawa da taron mata na Beijing
2020-02-26 12:01:35        cri
Hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD, ta kira wani taron manyan jami'anta, a jiya Talata, don tuna cika shekaru 25 na taron mata na duniya karo na hudu da majalisar ta shirya a shekarar 1995 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A jawabin da ta gabatar, babbar kwamishinar hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD Michelle Bachelet, ta bayyana taron mata na kasa da kasa na Beijing, a matsayin babban ci gaba a tarihi. A cewarta, yarjejeniyar Beijing da aka cimma game da harkokin mata, ta nuna yadda aka yi watsi da munanan al'adu, dake nuna cewa, ya kamata a magance yadda ake cin zarafin mata a cikin iyali, da yadda ake hana mata zuwa makaranta.

Ta ce, ko da yake, har yanzu duniya ba ta cimma daidaito a tsakanin jinsi ba, amma adadin matan dake aikin albashi ya karu, haka kuma sama da kasashe 140 sun alkawarta samar da daidaiton jinsi a kundin tsarin mulkin kasashensu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China