Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai karin mutane 334 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a Koriya ta Kudu
2020-02-27 16:07:51        cri

Yau Alhamis, hukumar kula da yaduwar cututtuka ta kasar Koriya ta Kudu ta fidda labari cewa, daga ranar 26 zuwa ranar 27 ga wata, akwai karin mutane 334 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19. Yanzu haka, majalisar dokokin kasar Koriya ta Kudu ta riga ta gyara dokar da abin ya shafa domin karfafa aikin hana yaduwar cutar.

Ya zuwa yanzu, gaba daya an tabbatar da mutane 1595 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19, yayin da mutane 12 suka mutu sakamakon cutar, kuma baki daya mutane 24 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China