Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 yana ci gaba da karuwa a kasashen Japan da Koriya ta Kudu
2020-02-24 12:11:21        cri
Kwanan baya, adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 yana ci gaba da karuwa a kasashen Koriya ta Kudu da Japan. A jiya kuma, gwamnatin kasar Koriya ta Kudu ta daga matsayin yin gargadi kan yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 zuwa matsayi na koli, wato "mafi tsanani".

Rahotanni daga hukumar yaki da cututtuka ta kasar Koriya ta Kudu na cewa, ya zuwa karfe 4 na yammacin jiya Lahadi, adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya karu zuwa 602, sa'an nan, wani ya mutu a daren jiya Lahadi, hakan ya sa, baki daya mutane 6 ne suka rasu sakamakon kamuwa da cutar a kasar Koriya ta Kudu.

A jiya da yamma kuma, shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya sanar da cewa, masu ba da shawara da masanan cututtuka masu yaduwa sun bukaci gwamnati da ta daga matsayin yin gargadi kan yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 zuwa matsayi na koli, da karfafa ayyukan yin kandagarki kan cutar. Sa'an nan, ma'aikatar ilmi ta kasar Koriya ta Kudu ta sanar da dakatar da lokacin bude makarantun reno da firamare da sakandare har zuwa mako guda wato zuwa ranar 9 ga watan Maris a duk fadin kasar.

A kasar Japan kuma, ya zuwa karfe 9 da minti 20 na daren ranar 23 ga wata, gaba daya, an tabbatar da cewa, mutane 838 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, ciki har da wasu 'yan kasar Japan da masu yawon shakatawa na kasar Sin guda 133, fasinjoji da ma'aikatan jirgin ruwa na "Diamond Princess" guda 691, da kuma mutane 14 da gwamnatin kasar Japan ta dawo da su kasar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China