Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar masana ilimin likitanci ta WHO za ta je Wuhan a yau
2020-02-22 16:12:50        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sanar yayin taron manema labarai da aka yi jiya a birnin Geneva cewa, tawagar masana ilimin likitanci ta hadin gwiwar WHO da kasar Sin, za ta je birnin Wuhan, inda cutar COVID-19 ta fara bulla, a yau Asabar, don gudanar da aiki.

Wadannan fitattun masanan sun fito ne daga kasashen Sin, Japan, Koriya ta Kudu, Singapore, Rasha, Jamus, Amurka da kuma Najeriya, wadanda masana ne a fannin ilmin likitancin cututtuka masu yaduwa, da kwayoyin cuta, da gudanar da aikin yaki da cututtuka a asibiti, da shawo kan annoba, da ma kiwon lafiyar jama'a. Yanzu suna bincike da nazarin da ya shafi cutar COVID-19 a kasar Sin, a kokarin samun wasu amsoshin da ba a kai ga ganowa ba tukuna, ciki har da karfin yaduwar kwayoyin cutar, da tasirin matakan da Sin ke dauka na dakile yaduwar cutar, da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, Tedros ya sanar a yayin taron cewar, ya riga ya nada sabbin manzannin musamman 6, domin zuwa kasashen duniya da nufin gudanar da aikin da ya shafi cutar COVID-19. A cewarsa, muhimmin aikin da WHO ke yi shi ne, daidaita matakan da duniya ta dauka na yaki da cutar, kuma sabbin manzannin na musamman za su taimaka wajen gudanar da aikin. Ya kuma sake yin kira ga kasa da kasa su yi amfani da lokacin da ya dace domin tinkarar cutar gaba daya.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China