Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar WHO ta isa Sin domin neman wasu bayanai game da COVID-19
2020-02-20 11:17:16        cri

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce wata tawagar kwararru ta hukumar, ta isa kasar Sin, inda za ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki game da wasu abubuwa masu nasaba da cutar numfashi ta COVID-19.

Mr. Tedros ya kuma ce, ya samu bayanai daga wakilai mambobin hukumar ta WHO, game da wasu muhimman abubuwa da suka shafi wannan cuta, ciki hadda bukatar sassan kasa da kasa, ta samar da tallafin tunkarar wannan annoba, wanda hakan zai kunshi samar da kudade ga tsarin kula da lafiyar al'umma a matakin al'umma, da kuma kudaden gudanar da bincike da samar da magunguna, wanda hakan zai ba da damar samar da kayayyakin aiki da ake bukata ga kasashe.

Daga nan sai babban jami'in na WHO ya godewa kasar Canada, bisa gudummawar ta a fannin yaki da cutar COVID-19, yana mai alkawarin ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya, wajen dakile yaduwar wannan annoba.

Kafin hakan dai, kasar Canada ta alkawarta samar da kudi da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 2 ga hukumar ta WHO, domin tallafawa aikin tunkarar wannan cuta ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China