Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Algeria ta tabbatar da samun bullar cutar COVID 19 na farko
2020-02-26 09:47:13        cri
Ministan lafiya na kasar Algeria, Abderrahmane Benbouzid, ya sanar da bullar cutar COVID-19 na farko a kasar.

Da yake jawabi ta tashar talabijin na ENTV ta kasar, Abderrahmane Benbouzid, ya ce wanda ya kamu da cutar dan kasar Italiya ne da ya isa Algeria a ranar 17 ga watan Fabreru tare da wani mutum, yana mai cewa tuni aka tura su asibitin Pasteur na birnin Algiers. Kuma bayan bincike, an tabbatar da daya daga cikinsu na dauke da cutar numfashi ta COVID-19.

Ya kara da cewa, nan take aka kebe mara lafiyan, inda ake ba shi kulawa ta musammam.

Har ila yau, ministan ya tabbatar da cewa an dauki matakan kariya a filayen jiragen sama da tasoshin ruwa da iyakokin kasa, ciki har da kafa kamarori masu auna zafin jiki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China