Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sassauta matakin gaggawa na yaki da annobar cutar COVID-19 a wasu sassan kasar Sin
2020-02-24 13:33:49        cri
Kwanan baya, an sassauta matakin gaggawa na yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a wasu wuraren kasar Sin bisa dokokin kasar da kuma halin da ake ciki a wadannan wurare a fannin yaki da annobar.

Daga karfe 12 na tsakar daren jiya ne mahukuntan lardin Shanxi suka daidaita matakin gaggawa na tinkarar al'amuran ba-zata da suka shafi lafiyar al'umma daga mataki na farko zuwa mataki na 2. Yayin da, mahukuntan lardin Yunnan suka daidaita matakin zuwa na 3 a maimakon na farko. Haka zalika, a lardin Guangdong, an daidaita matakin zuwa na 2 a maimakon na farko tun daga karfe 9 na safiyar Litinin 24 ga wata.(Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China