Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi zai ziyarci Uganda Congo da Senegal
2019-12-16 19:27:45        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya tabbatar da cewa, mamban kwamitin koli na hukumar siyasa ta JKS Yang Jiechi, zai ziyarci Uganda, da jamhuriyar Congo da Senegal, tsakanin ranekun 17 zuwa 22 ga watan Disambar shekarar nan.

Yang wanda kuma shi ne daraktan ofishin kwamitin harkokin wajen na kwamitin kolin JKS, zai yi musayar ra'ayoyi tare da jami'an gwamnatocin kasashen 3, game da batutuwan da suka shafi inganta kawancensu, da ingiza aiwatar da sakamakon da aka cimma, yayin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC, tare da tattaunawa game da al'amuran shiyya-shiyya da na kasa da kasa dake jawo hankalin sassan. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China