Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba za a iya rusa alaka a tsakanin Sin da Afirka ba
2020-02-07 19:18:22        cri
Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Jumma'a ta kafar Intanet cewa, duk mai neman tayar da matsala tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ba zai yi nasara ba.

Kafofin yada labaru na ketare sun ruwaito jami'an kasar Amurka na cewa, gwamnatin Amurka tana fatan hana gwamnatin Sin ta taimaka wa kasashen Afirka su kafa cibiyoyin yin rigakafin cututtuka, da sunan wai kasar Sin tana neman yin leken asirin kimiyya.

Dangane da hakan, madam Hua ta ce, kalamin ba shi da tushe sam. Kiwon lafiya na da muhimmanci a fannin yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Ya zuwa yanzu kasar Sin ta tura likitoci da nas-nas dubu 21 zuwa kasashen Afirka, inda suka taimaka mazauna wurin miliyan 220. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China