Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin: Wasu kasashe na fuska biyu kan matakan yaki da ta'addanci
2019-12-04 10:42:44        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, ta'addanci babbar matsala ce dake damun dukkan kasashen duniya, don haka bai dace a rika yin fuska biyu kan wannan batu ba, kamar yadda wasu kasashe ke nunawa a zahiri.

Rahotanni na cewa, 'yan sandan Burtaniya sun yi nasarar kama da ma kashe mutumin da ake zargi da kai harin ta'addanci na baya-bayan a birnin London. Koda yake, a baya bangaren Burtaniya, ya zargi 'yan sandan yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin da amfani da doka kan masu tayar da bore, inda karara ya nuna fuska biyu.

Kafofin watsa labarai na kasar Burtaniya sun bayyana cewa, gwamnatin Burtaniya ta kafa wata kungiya ta musamman ga wadanda ke ta hannu a ayyukan ta'addanci, wato shirin "Turjiya da kwance damara (DDP) tare da sanya ido kan jami'an da abin ya shafa."

Koda yake, shirin na DDP bai hana kai hare-haren ta'addanci ba. Mutumin da ya kai harin ta'addanci a birnin London ranar 29 ga watan Nuwanban, dalibin shirin ne na shekaru 8.

Madam Hua Chunying ta bayyana a taron manema labarai da aka gudanar ranar 3 ga watan Disamban, kan tambayar da aka yi mata cewa, baya ga Burtaniya da sauran kasashe, sama da kasashe 20 sun bullo da irin wadannan shirye-shirye na tilas ga wadanda ake zargi da aikata ta'addanci. Da farko manufar wadannan shirye-shirye, daya ne da ta cibiyar koyar da sana'o'i dake yankin Xinjiang. Koda yake, matakan kafa cibiyar samar da horo dake yankin na Xinjiang sun fi tsari da kuma yin tasiri. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China