Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MFA: Ko akwai alaka tsakanin yarjejeniyar Sin da Birtaniya da Amurka?
2019-12-04 10:34:44        cri
Yayin wani taron manema labarai a jiya Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin MFA, Hua Chunying, ta musanta tsokacin sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, game da yarjejniyar Sin da Birtaniya.

Hua Chunying ta jaddada cewa, ka'idoji da manufofin HK dake cikin yarjejeniyar da sauran wasu batutuwa, matsaya ce da kasar Sin ta dauka da kanta, wanda batu ne na cikin gidanta, ba wai tanadi ne na yarjejeniyar da ta cimma da Birtaniya ba. Ta ce dokar aiwatar da manufar "kasa daya mai tsarin mulki 2" a HK, tanadi na kundin tsarin mulkin kasar Sin.

Rahotanni sun ce, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya bayyana a baya-bayan nan cewa, yarjejeniyar Sin da Birtaniya, yarjejeniya ce da MDD ta amince da ita, kuma Amurka na fatan tabbatar da sahihancin alkawurran dake cikin yarjejeniyar. Ya ce Amurka na bukatar Sin ta samo mafita bisa girmama manufar "kasa daya mai tsarin mulki 2"

Hua Chunying ta yi nuni da cewa, Amurka na ta kokarin yayata abun da ta kira da demokradiyya da 'yanci da hakkin bil adama a fadin duniya, amma ta yi watsi da matsalolin demokradiyya da 'yanci da hakkokin bil adama a kasarta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China