Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Sanarwar da Amurka ta fitar game da yankin Xinjiang zargi ne na siyasa da tarin karairayi
2019-11-27 19:35:27        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau cewa, bayanan da wasu masu fada a ji daga Amurka suka yi kan yankin Xinjiang, zargi ne na siyasa da kuma tarin karya, inda suka sake nuna yadda suke yin fuska biyu game da yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Geng ya ce, gwamnatin kasar Sin tana kare 'yancin bin addinai na Sinawa, ciki har da 'yan Uygur dake Xinjiang da sauran kananan kabilu bisa doka. Haka kuma kasar Sin tana maraba da baki 'yan kasashen waje wadanda suke martaba manufar fadin gaskiya da adalci, da su ziyarci yankin na Xinjiang, don gane ma idonsu.

A jiya ne dai sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya bayyana cewa, wasu rahotanni da aka wallafa a kwanakin baya, sun nuna cewa, ana take hakkin bil-Adama a yankin na Xinjiang, inda ya bukaci gwamnatin Sin da ta saki dukkan wadanda take tsare da su. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China