![]() |
|
2020-02-25 12:30:53 cri |
Roseline Kihumba, mukadashin shugabar sashen ci gaban harkokin Intanet da cudanya na gidauniyar hadin gwiwar tallafawa masu yawan shekaru ta kasa da kasa, ta bayyana cewa, ya kamata gwamnatocin Afrika su amince da shirin shigar da tsoffi masu yawan shekaru cikin ajandar dawwamamman ci gaban nahiyar.
Kihumba ta bayyana cikin wata sanarwar da aka fitar a Nairobi cewa, aiwatar da shirin samar da dawwammman ci gaba na (SDGs) da ajandar bunkasa Afrika nan da shekarar 2063 za su biya muradu da kuma kare hakkin mutane masu yawan shekaru.
Ana sa ran batun matsalolin tsofaffi shi ne zai mamaye tattaunawar taron dandalin samar da dawwamamman ci gaban Afrika na shiyya karo na shida wanda za'a gudanar a wannan mako a birnin Harare, na kasar Zimbabwe.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China