Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kafa gwamnatin hadin kan kasa a Sudan ta kudu
2020-02-23 16:03:18        cri
A jiyar Asabar an kafa gwamnatin hadin kan kasa a Sudan ta kudu, kasa mafi sabunta a duniya bayan shafe shekaru ana yakin basasa a kasar ta nahiyar Afrika.

Riek Machar, tsohon madungun 'yan tawayen kasar Sudan ta kudu, a ranar Asabar an rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban kasa na sabuwar gwamnatin hadin kan kasar.

Machar an rantsar da shi tare da wasu sabbin mataimakan shugaban kasar uku, da suka hada da Taban Deng Gai, James Wani Igga da Rebecca Nyandeng De Mabior, a bikin da aka gudanar a Juba wanda ya samu halartar wasu shugabannin shiyyar.

Machar, wanda ya kasance jagoran 'yan tawayen (SPLM-IO), shugaban kasar Silva Kiir ya nada shi a matsayin sabon shugaban kasar a ranar Juma'a gabanin gudanar da shagalin bikin nadin.

A jawabin da ya gabatar bayan rantsar da shi, Machar ya ce, zai yi aiki tare da Kiir da sauran shugabanni wajen kawo zaman lafiya a kasar kana ya godewa dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen shirin maido da zaman lafiyar kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China