Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Afrika na hada hannu da takwararta ta kasar Sin domin yaki da cutar numfashi ta Coronavirus
2020-01-29 16:27:43        cri
Cibiyar takaita yaduwar cututtuka (CDC) ta Afrika, na hada hannu da takwararta ta kasar Sin domin dakile yaduwar cutar numfashi da kwayar cutar Coronavirus ke haddasawa a nahiyar Afrika, bayan an gano wani da ake zaton ya kamu da cutar.

Daraktan cibiyar CDC na Afrika John Nkengasong, ya shaidawa manema labarai a hedkwatar AU cewa, Cibiyar na hada hannu da bangarori daban-daban, ciki har da cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar Sin, game da barkewar kwayar cutar Coronavirus, da ta fara bulla a kasar.

Daraktan ya ce tuni aka fara amfani da tsarin tunkarar matsalar gaggawa ta AU da nufin dakile yaduwar cutar a nahiyar.

Da yake tsokaci kan Cote d'Ivoire da aka gano wani da ake zaton ya kamu da cutar, John Nkengasong, ya ce cibiyar CDC na tuntubar hukumomi a kasar.

Har ila yau, da yake jadadda yadda kwayar cutar Coronavirus ke saurin bazuwa, daraktan ya yabawa matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen tunkarar yanayin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China