Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru sun bukaci a bunkasa tattalin arzikin Afrika ta hanyar shiga WTO da aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA
2020-02-14 11:48:50        cri
Kwararrun tattalin arzikin Afrika da masu tsara dabarun shugabanci da suka halarci taron tattaunawa na shiyya game da batun shiga kungiyar ciniki ta duniya WTO sun jaddada bukatar a zurfafa hanyoyin bunkasa tattalin arziki nahiyar ta hanyar shiga kungiyar WTO da kuma aiwatar da yarjejeniyar ciniki maras shinge ta nahiyar wato AfCFTA.

Masanan sun yi kiran a zurfafa ci gaban tattalin arzikin nahiyar ne a lokacin taron shiyya karo na uku game da yadda Afrika za ta samu wakilci a WTO, wanda aka tsara gudanarwa tsakanin 12 zuwa 14 ga watan Fabrairu, a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, taken taron shi ne "Zurfafa hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Afrika ta hanyar zama mamba a WTO da aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA."

Albert Muchanga, kwamishinan AU na sashen ciniki da masana'antu, ya fada a babban taron nahiyar cewa, Afrika tana goyon bayan tsarin gamayyar bangarori daban daban na duniya, a yayin da ake samun ra'ayain kariya daga wasu sannan duniya.

Stephen Karingi, daraktan shiyya mai kula da harkokin ciniki a hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD wato UNECA, ya yi tsokaci game da batun tsarin gudanarwar ciniki na kasa da kasa, wanda ya shafi Afrika ta wani bangaren, kana ya shafi wasu yankunan yammacin duniya ta wani bangaren.

Jami'in hukumar UNECA ya kara da cewa, duk da kasancewa wasu sassan duniya suna yin kafar ungulu ga tsarin bangarori daban daban na dokokin diflomasiyya, amma Afrika tana kara nanata aniyarta ta goyon bayan tsarin tattalin arziki mai 'yanci a matsayin tsarin da zai kara bunkasa ci gaban al'ummar duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China