Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutanen da suka mutu a harin bam cikin babbar mota a Mogadishu ya kai 76
2019-12-28 20:33:05        cri
Kimanin mutane 76 ne suka mutu kana wasu gwammai suka jikkata a wani shingen binciken tsaro mai fama da yawan jama'a a Mogadishu, babban birnin kasar Somali a yau Asabar, wata kungiyar bada agajin lafiya ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kungiyar bada agajin lafiyar ta Aamin Ambulance, wacce ta gudanar da aikin ceton kuma ta tabbatar da mutuwar adadin mutanen, tana mai cewa, wasu mutanen 70 da suka samu raunuka an garzaya dasu asibitin Mogadishu domin basu kulawa.

Sai dai kuma, magajin garin Mogadishu Omar Filish yace, mutane 90 ne suka samu raunuka a harin bam din babbar motar. Amma bai ambata adadin mutanen da suka mutu ba, magajin garin ya ce motar tana kan hanyar zuwa cikin birnin Mogadishu ne sai jami'an tsaro suka tsayar da ita a wajen binciken ababen hawa dake yammacin Mogadishu.

Filish yace mafi yawan mutanen da harin ya rutsa dasu daliban jami'ar Banadir ne a Mogadishu.

Babu wata kungiyar data dauki alhakin kai harin. Amma kungiyar al-Shabab mai alaka da Al-Qaida ta sha kaddamar da makamantan wadannan hare hare duk da yunkurin da aka yi na fatattakar kungiyar daga Mogadishu a shekarar 2011.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China